MASARAUTAR ZAZZAU,MUTANE 8 NA HANKORON DAREWA KAN KARAGA
Saraurar Zazzau: Mutane 8 Na Hankoron Darewa Kan Karaga
Akalla mutane takwas ne daga gidajen sarautar Zazzau daban-daban suke hankoron darewa kan karaga domin maye gurbin tsohon sarki, marigayi Alhaji Shehu Idris.
Aminiya ta gano cewa ya zuwa yammacin ranar Alhamis da misalin karfe 5:00 na yamma wanda shine lokacin da masu zabar sarkin su ka saka a matsayin wa’adi na karshe, akalla mutum takwas sun nuna sha’awar sarautar.
Daga baya kuma wani daga cikin ‘yan sarautar ya yi korafin cewa ba shi da masaniyar a jiyan za a rufe, kafin daga bisani shima aka karbi takardarsa wanda hakan kenan ya mayar da adadinsu ya koma takwas kenan.
A cewar wata majiya dai, sharadin da masu zabar sarki suka saka shine a inda kowanne gidan sarauta ya gaza cimma matsayar fito da mutum daya, to za su iya tsayar da mutanen da yawansu ba zai haura uku ba a matsayin ‘yan takara.
Majiyar ta kara da cewa, “Saboda haka yanzu uku daga cikin gidajen sarautar Zazzau hudu ne su ka tsayar da ‘yan takara su na bukatar samar da sarkin Zazzau na 19.
“Gidan Katsinawa, inda daga nan ne tsohon sarki ya fito suna da ‘yan takara hudu; Wamban Zazzau, Alhaji Abdulkareem Aminu, Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu; Dangaladiman Zazzau, Alhaji Aminu Idris da kuma Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris,” inji majiyar.
Daga gidan sarautar Mallawa kuwa, Aminiya ta gano cewa mutum uku ne ke son zama sarkin wadanda suka hada da Ciroman Zazzau, Alhaji Sa’idu Mailafiya; Barden Kudun Zazzau, Alhaji Shehu Tijjani da kuma Magajin Garin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli.
Sai dai Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jafaru ne kadai ya ke takara daga gidan sarautar Bare-bari, inji majiyar tamu.
A wani labarin kuma, a ranar Laraba ne masarautar Zazzau ta rubuta wasika a hukumance zuwa ga gwamnatin jihar Kaduna tana sanar da ita labarin mutuwar tsohon sarkin.
Hakan dai na nufin da rubuta wannnan wasikar, an fara bin matakan nada sabon sarkin a hukumance.
Ana sa ran dai gwamnatin ta rubuta amsar wasikar wacce za ta kunshi mataka
Comments
Post a Comment