Ku Rabu Da Zaɓen Jihar Ondo Ku Zo Ku Yaƙi Boko Haram
Ku Rabu Da Zaɓen Jihar Ondo Ku Zo Ku Yaƙi Boko Haram Daga Jaridar Idon Mikiya. Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya shawarci Sojoji su rabu da shirin bayar da tsaro a zaben jihar Ondo na ranar Asabar, 10 ga Oktoba, su fuskanci 'yan ta'addan Boko Haram a Arewa maso gabas. Zulum ya bayyana hakan ne a taron babban hafsan Sojin Najeriya daya gudana ranar Talata, 6 ga watan Oktoba a Maiduguri, birnin jihar Borno. Zulum ya ce ya yi mamaki lokacin da Buratai ya ke alfaharin nasarar da Sojoji suka samu wajen bayar da tsaro a zaben gwamnan jihar Edo kuma suna shirin maimaita hakan a zaben jihar Ondo. "Lokacin da babban hafsan Soji yayi magana da nasarar da suka samu a zaben Edo da kuma shirin na Ondo, abin ya ban tsoro saboda ina son Sojojin Najeriya su mayar da hankali wajen yaƙin yan ta'adda". Inji Zulum Zulum ya buƙaci Sojojin su fara shiga lungu da sakon yankin domin sabawa da mutane saboda a yarda da su yayin da suke gudanar da ayyukansu. Ya yi kira ga Sojojin su ...
Comments
Post a Comment